Home Labarai Haɗari matafiyan Kano suka yi ba ƴanbindiga suka kashe su ba

Haɗari matafiyan Kano suka yi ba ƴanbindiga suka kashe su ba

102
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta ƙaryata labarin da ake yaɗa wa cewa ƴanbindiga sun kashe wasu matafiya ƴan asalin jihar Kano su 16 kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wata sanarwa da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce mutanen sun yi hatsari ne a yankin Rigachikun da ke hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Hoton motar fasinjojin bayan ta faɗa rami

Gwamnatin ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da kuma addu’ar samun lafiya ga waɗanda suka samu raunika.

A ranar Alhamis ne dai wani labari ya riƙa yawo a kafafen intanet cewa ƴanbindiga sun kashe wasu matafiya ƴan asalin jihar Kano a hanyar Abuja-Kaduna.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply