Home Labarai Hadarin tankar mai ya hallaka rayuka a Lokoja

Hadarin tankar mai ya hallaka rayuka a Lokoja

138
0
gobarar

Hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC, reshen jihar Kogi, ta tabbatar da rasuwar mutane ashirin da uku a wani mummunan hadarin tankar dakon mai da ya auku da safiyar ranar Larabar nan akan hanyar Felele – Nataco kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a jihar Kogi.

Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa na Jihar, Mista Idris Ali ya shaida wa ‘yan jarida cewa wadanda abin ya shafa sun hada da magidanta maza goma, sai mata 9, sai kuma yara hudu da kunar wuta ta hana a gane jinsinsu.

Tuni dai, gwamnan jihar ta Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya nuna alhininsa game da wannan mummunan hadari na tankar dakon mai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply