Home Lafiya Hadin kai a tsakanin likitoci zai kawo ci gaban kiwon lafiya a...

Hadin kai a tsakanin likitoci zai kawo ci gaban kiwon lafiya a Nijeriya-Minista

81
0

 Saleem Ashir Mahuta

 

Karamin Ministan Lafiya a Nijeriya Dr. Adeleke Mamora ya shawarci ma’aikatan lafiya da su yi aiki cikin hadin kai domin samar da wadataccen aikin kula da lafiya a Kasar.

 

Dr. Mamora ya ce akwai bukatar ya yi wannan kiran duba da cewar hadin kan ma’aikatan lafiyar zai yi matukar taimakawa wajen samar da kula da lafiya da kuma ci gaban kasar.

 

Ministan na magana ne a yayin wani taro na ‘Makon Lafiya na shekarar 2018’ da Babban Asibitin Tarayya da ke Keffi a jihar Nasarawa ya shirya mai taken “Iska na da  muhimmanci ga rayuwa”

 

Mataimakin gwamnan Jihar Emmanuel Akabe a wurin taron ya ce, gwamnatin jihar za ta ci gaba wajen taimakon cibiyar domin samar da ayyukan kula da lafiya yadda ya kamata.

 

Daraktan Lafiya na Asibitin Dr. Yahaya Adamu a lokacin da ya ke jawabi, ya bayyana cewar cibiyar ta kara bude tare da daukaka darajar wani wurin samar da iska domin ganin marasa lafiya sun samu wadatattar iskar, yana mai zayyana wuraren da aka sanya bututun iskar(oxygen) daga wurin samar da iskar zuwa bangaren masu haihuwa, wurin kula da kananan yara da kuma wurin da aka ware na musamman domin kulawa da marasa lafiya da sauran su.

 

Adamu ya kuma bayyana cewar cibiyar ta kuma samar tare da sanya manyan injinan bayar da wutar lantarki masu karfin KVA 250 da Kuma 275 kari da wadancan da ake amfani da su domin daukaka samar da wutar lantarki a cibiyar.

 

Sai dai,  ya kuma bayyana rashin isassun kudi a matsayin matsalar da ta dakile rashin canza na’ura mai kwakwalwa domin gudanar da ajiye bayanan marasa lafiya na zamani a cibiyar yadda ya kamata.

 

 

Trust:          Saleem/Jani

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply