Abdullahi Garba Jani
Hukumar kula da alhazai ta jihar Kaduna ta ce ta kammala kwaso alhazanta 3,544 daga kasar Saudiyya wadanda suka gudanar da aikin hajjin bana.
A wata takarda da jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Abdullahi ya fitar, ta ce sawun karshe na dauke da alhazai 390 da suka iso Kaduna a ranar Asabar din nan.
Malam Abdullahi Yunusa ya ce saukar wannan jirgin a Kaduna ne ya alamta kawo karshen jigilar alhazan jihar Kaduna daga aikin hajjin bana a kasar Saudi Arabia.
A lokacin aikin jigilar alhazan, kamfanoni biyu na Max Air da na Fly Nas ne suka gudanar da aikin, inda Max Air ya kwaso alhazai 2,710 sai Fly Nas ya kwaso 834.
Jaridar Vanguard ta ba da labarin cewa alhazai 3,545 ne suka gudanar da aikin hajjin bana daga jihar Kaduna, inda daga cikinsu daya ne ya rasa ransa a can kasar Saudi Arabia.
Vgd: Jani/dkura
