Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Hana bara: Gwamnatin Kano ta tallafi mata da matasa

Hana bara: Gwamnatin Kano ta tallafi mata da matasa

19
0

Biyo bayan hana barace-barace kan titunan jihar, gwamnatin jihar Kano ta horas da akalla mata da matasa 60 sana’o’i daban-daban domin su zamo masu dogaro da kai.

Da take magana lokacin rabon kayan tallafin da aka ba wadanda suka amfana da horon a Birnin Kano, Kwamishinar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar Dr Zahara’u Muhammad Umar, ta ce akwai bukatar mata su samu tallafi da wadatar kudi domin tallafawa iyalansu.

Kwamishinar ta ce da yawa daga cikin matan da suka amfana da shirin an dauko su ne daga kan titunan jihar.

Ta ce wannan ne ya wajabta wa gwamnatin daukar matakin tallafawa matan da sauran masu karamin karfi a jihar domin su zama masu dogaro da kan su.

Wadanda suka amfana da shirin dai sun samu tallafin Naira 10,000 ko wannensu, baya ga tallafin kekunan dinki, farin wake, waken suya, gero, firiza, shinkafa, kananan injinan janareto, injinan saka, kayan gwanjo da dai sauransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply