Home Labarai Hana kiwo: An cimma matsaya tsakanin gwamnoni da Miyetti Allah

Hana kiwo: An cimma matsaya tsakanin gwamnoni da Miyetti Allah

49
0

Ƙungiyar gwamnonin Nijeriya da ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah sun cimma matsaya kan hana kiwon dare da share wuri zauna a dazukan kudu maso Yammacin Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba.

Wata sanarwar bayan taro kan sha’anin tsaro da gwamnonin, Miyetti Allah da kuma shugabannin hukumomin tsaro suka gudanar a ranar Litinin, sun kuma amince da haramta wa ƙananan yara kiwo.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya rawaito cewa gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da na jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu, Abubakar Atiku Bagudu na Kebbi, Muhammad Abubakar Jigawa, Gboyega Oyetola na Osun, Seyi Makinde na Oyo, sai tsohon mataimakin gwamnan Osun Sanata Iyiola Omisore.

Da yake karanta takardar bayan taron, Gwamnan Ekiti kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Kayode Fayemi ya ce dole ne a dakatar da kiwon kara zube domin kaucewa rikicin manoma da makiyaya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply