Home Labarai Har yanzu akwai masu amsar fanshon Naira dubu 4,000 a Nijeriya in...

Har yanzu akwai masu amsar fanshon Naira dubu 4,000 a Nijeriya in ji ‘yan fansho

84
0

Wasu tsoffin ma’aikatan gwamanatin tarayyar Nijeriya, sun koka game da abin da suka kira mayar da su saniyar ware da gwamanatin kasar ta yi dangane da tsarin fanshonsu.

Tsoffin ma’aikatan suka yi zargin cewa har yanzu daga cikinsu akwai masu amsar fanshon Naira dubu 4,000 a duk wata.

Hakan kamar yadda suka ce, ya biyo bayan kin daga darajar fanshonsu da gwamanatin tarayyar kasar ta yi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadas a duk bayan shekaru biyar.

A cikin wata takarda daga daga shugaban kungiyar ‘yan fansho na kasa Mr Sunday Omezi, ta ce ‘yan fanshon sun roki gwamanatin tarayya da ta mayar da fanshon na su daga Naira dubu 4,000 zuwa ko da Naira dubu 25,000 ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply