Ma’awiyya Abubakar Sadiq
wani mataki na kara daukar matakan kauce wa yaduwar cutar Corona, mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya tattauna da Uwayen kasa guda tamanin da shida a fadar sa.
Taron tattaunawar dai ya tabo batun rashin jin dadi da sarki ya nuna game da har yanzu wasu ba su yadda ma akwai cutar ba duk kuwa da irin alkalumma mutanen da take kashewa duniya baki dai.
A saboda haka ne, sarkin ya wayar da kan Uwayen kasar da su ci gaba da wayar da kan al’umma kan wannan cuta cewa gaskiya ce.
Sarkin yace ma Uwayen kasar su kara sanya ido kan shige da fice don gudun kada wani ya kwaso ta ya shigo da ita, yace dokar hana shige da fice da gwamnati ta saka, su tabbatar da ita ta hanyar isar da sakon don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
