Home Labarai Har yanzu APCn Zamfara a hargitse take – Marafa

Har yanzu APCn Zamfara a hargitse take – Marafa

91
0

Sanata Kabiru Marafa jigo a jam’iyyar APC ta jihar Zamfara yace babu kanshin gaskiya a kalaman Gwamna Mai Mala Buni da ya ke cewa an warware matsalolin APC a jihar.

Gwamna Mai Mala wanda shi ne shugaban kwamitin riko na APC na kasa, ya yi ikirarin cewa an warware matsalolin da APC ke fuskanta a jihohin Zamfara, Cross Rivers, Ondo, Oyo, Bayelsa, Bauchi, Ekiti, da Enugu.

A cikin wata takardar martani da Sanata Marafa ya fitar, ya ce rikicin jam’iyyar na jihar na nan daram.

Ya ce har yanzu kwamitin da aka kafa bai yi komai ba, ya kara jaddada cewa har yanzu kan ‘ya’yan jam’iyyar a rarrabe ya ke.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply