Home Lafiya Har yanzu ban warke daga Covid-19 ba – El-Rufa’i

Har yanzu ban warke daga Covid-19 ba – El-Rufa’i

76
0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ce har yanzu bai warke daga cutar Covid-19 da ya kamu da ita ba, wadda yanzu haka ta kama sama da mutane 373 a Nijeriya.

Gwamnan ya faɗi haka ne bayan ya jagoranci zaman majalisar zartaswar jihar a jiya Laraba.

Da yake magana a shafin sa na Twitter El-Rufa’i ya gargaɗi masu ƙoƙarin mayar da fari baƙi kan yanayin cutar tasa.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa zai sanar da halin da yake ciki da kan sa, da zaran ya warke daga cutar.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 28 ga watan Maris ne, gwamnan ya bada sanarwar ya kamu da cutar.

Saidai ba kamar sauran manyan mutanen da suka kamu da cutar kuma suka warke ba, El-Rufa’i ya ce har yanzu yana ɗauke da cutar, bayan shafe makonni biyu da ya yi a keɓance.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply