Home Labarai Har yanzu da sauran rina a kaba a sha’anin tsaron Katsina –...

Har yanzu da sauran rina a kaba a sha’anin tsaron Katsina – Masari

193
0

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya ja kunnen al’ummar da ke fama da hare-haren ta’addanci da su guji bayar da bayanan sirri game da yankunansu ga ‘yan ta’adda, su kuma rika tona asirin duk masu irin wannan dabi’a ta infoma.

Masari ya yi wannan jan kunne ne a lokacin wata zantawa da gidan rediyon Nijeriya na Kaduna.

Ya kuma bayyana cewa ya lura ana samun ci gaba a harkar samar da tsaro a yankunan da ke fama ta matsalolin tsaro. Sai dai ya ce duk da abin yana lafawa, amma ba a kai ga biyan bukata ba.

Ya bayyana fatar cewa tsare-tsaren da aka yi yanzu za su kai a samu cikkaken zaman lafiya kamar yadda aka sani a da.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply