Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya ce har yanzu yana yin shawarwari da masu ruwa da tsaki kafin ya yanke shawarar matakin siyasar da zai ɗauka a gaba.
Rahotan jaridar Daily Trust ya ruwaito shugabannin siyasa daga jam’iyyun PDP da ADC na ƙoƙarin shawo kan Goje ya koma jam’iyyunsu, bayan da ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba ta ba shi tikitin neman komawa majalisar dattawa ba.
Da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa da suka taru a gidansa da ke Gombe ranar Asabar, Goje ya musanta rahotannin cewa ya sauya sheka daga APC zuwa wata jam’iyyar siyasa a kasar.
Sanatan ya ce har yanzu yana cikin APC, amma zai sanar da magoya bayansa matakin siyasar da zai ɗauka nan ba da jimawa ba. Ya kuma bukaci su ci gaba da biyayya ga shugabannin jam’iyyar tare da jiran ƙarin bayani daga gare shi.
Goje, wanda ke kan wa’adinsa na huɗu a majalisar dattawa, ya kuma shawarci magoya bayansa da su koma sansanoninsu su jira umarninsa na gaba.
Da yake waiwayar kusan shekaru 45 da ya shafe a siyasa, Goje ya ce ya taɓa tsayawa takara sau takwas tun daga zamanin jamhuriya ta biyu zuwa yanzu, kuma ya samu nasara a dukkan zaɓukan da ya shiga ba tare da shan kaye ba.
Ya ce a tsawon wannan lokaci ya riƙe mukamin ɗan majalisar dokokin jihar, ya zama gwamnan Gombe na tsawon wa’adi biyu, sannan ya lashe zaɓen majalisar dattawa sau huɗu. Haka kuma, ya kasance ministan Nijeriya tsakanin shekarar 1999 zuwa 2001.
Goje ya bayyana cewa a shekarar 2019 ya sanar da yin ritaya daga siyasa, kuma ya ce ba zai sake neman takara a zaɓen 2023 ba. Sai dai ya ce matsin lamba daga magoya bayansa ya sa ya sake shiga takara a 2023.
Kwamitin zaɓen fidda gwani na APC na majalisar wakilai da majalisar dattawa a jihar Gombe ne ya ayyana DCP Mohammed Ahmed mai ritaya a matsayin wanda ya lashe tikitin neman kujerar majalisar dattawa mai wakiltar Gombe ta tsakiya.
A halin yanzu, Goje bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara ƙoƙarin jawo manyan ‘yan siyasa zuwa sansanoninsu gabanin babban zaɓen 2027.
