Home Coronavirus Har yanzu mutane ba su yarda da Covid-19 ba a Borno –...

Har yanzu mutane ba su yarda da Covid-19 ba a Borno – Kadafur

65
0

Mataimakin gwamnan jihar Borno Umar Kadafur ya koka kan yadda jama’ar jihar ke nuna shakku ga samuwar Covid-19, kamar yadda suka riƙa nuna ko in kula a kan Boko Haram.

Kadafur wanda shi ne shugaban kwamitin yaƙi da cutar a jihar ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi.

Ya yi nadamar cewa, duk da yadda cutar ke yaɗuwa a jihar, amma har yanzu mutane da dama ba su yarda akwai cutar ba.

Kadafur ya bayyana takaicin sa kan yadda jama’a ke halartar sallolin jana’iza da na farilla ba tare da la’akari da bada tazara ba.

Ya ce lokacin da Boko Haram ta faro mutane da dama ba su ɗauki abun da muhimmanci ba saidai komai ya lalace, yana mai cewa wannan cutar ita ma wata Bokon Haram ce.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply