Home Labarai HARAJI: Jihar Kaduna ta tara Naira bilyan 30.3 a watanni goma

HARAJI: Jihar Kaduna ta tara Naira bilyan 30.3 a watanni goma

81
0

SHARIFUDEEN IBRAHIM MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tara kudi Naira bilyan 30.3 a matsayin Kud’aden shiga cikin watanni goma.

Hukumar tattara harajin cikin gida ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa tara yawan a matsayin kudaden shiga cikin watanni goma wani abin a yaba ne.

Shugaban Hukumar tattara harajin cikin gida na Jihar Kaduna, Dokta Sa’id Abubakar ya bayyana hakan ga Kamfanin dillancin labaran Nijeriya a Kaduna.

Dokta Abubakar ya danganta samun wannan kudade masu yawa ga tsare-tsaren da hukumar ta samar da kuma hadin gwiwa da kamfanonin tattara haraji.

Bugu da kari, Shugaban yace nan ba da jimawa ba, hukumar za ta samar da hanyar biyan haraji mafi sauki ba tare da an sha wahala ba.

Har ila yau yace nan ba da jimawa ba hukumar za ta fara ganawa da masu biyan haraji da nufin samun hadin kansu wajen biyan haraji ba tare da an tirsasasu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply