Home Kasashen Ketare Harbi kan ‘mai uwa da wabi’ a jihar Texas ya tayar da...

Harbi kan ‘mai uwa da wabi’ a jihar Texas ya tayar da hankalin Amirkawa

60
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

 

Mutane 5 sun rasa rayukansu, a yayin da 21 suka samu  raunuka a wani hari da aka kai a jihar Texas ta ƙasar Amirka.

Gidan talabijin na CNN ya bayar da wannan labari yana mai cewa akwai jarirai guda biyu da kuma wasu mutane bakwai da ke cikin rai-kwa-kwai-mutu-kwa-kwai harbe-harben suka shafa

Jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin dakatar da maharbin wanda yake a cikin mota, a daidai nan ne ya samu damar ƙwace wata mota ta kamfanin aikawa da wasiku ya ci gaba da tuƙa motar zuwa cikin garin Odessa yana ɓarin wuta akan jama’a, kamar yanda ƴan sanda  suka bayyana.

 

Ƴan sanda dai sun gano cewa wanda ake zargin farar fatane ɗan kimanin shekara 30, amma dai basu gano sunan shi ba, kuma ba su gano dalilin da yasa ya aikata wannan harin ba.

 

Da farko jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin tsaida motar a daidai wata maraba da ake kira ’20 highway’, amma kafin motar ta tsaya sai  direban wanda shi kaɗai ne acikin ta ya fiddo bakin bindiga ta tagar motar ta baya ya fara sakin harbi ga jami’an tsaron DPS patrol unit, kamar yadda hukuma mai kula da lafiyar jama’a ta bayyana .

Donald trump Shugaban kasar Amirka

An dai jiwa daya daga cikin jami’an tsaron rauni, daga bisani maharin ya gudu yabar wurin, inda ya ci gaba da harba bindaga akan jama’ar da basu ji ba basu gani ba .

 

Wasu harbe-harben  yayi  sune a babbar hanyar da ta hada biranan Odessa da Midland inda aka ga motocin da ya harba da ramukan harsasai .

 

Yan sanda dai sun ce maharin ya rasa ran shi ne adaidai lokacin da ake musayar wuta tsakanin shi da jami’an tsaro, adaidai bakin gidan kallo na Odessa.

 

Shugaban kasar Amirka Donal Trump, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar, Attorney General Bill Barr, ya sanar da shi faruwar lamarin

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply