Home Labarai Hare-haren ‘yan bindiga sun sa an kafa kungiyar Banga a Illela ta...

Hare-haren ‘yan bindiga sun sa an kafa kungiyar Banga a Illela ta jihar Sakkwato

64
0

Jama’ar garin Illela ta jihar Sakkwato sun samar da wata babbar kungiyar Banga ta sintiri da ke gudanar da aikin samar da tsaro da zarar dare ya yi don kare kansu daga aika-aikar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Su dai mutanen wannan garin da ke bakin iyakar Nijeriya da Nijar, na da harkokin kasuwanci da masu kudi sosai, abin da ya fara jan hankalin masu garkuwa da mutane karkata akalar su zuwa garin, inda suka fara daukar manyan masu kudi don neman kudin fansa a cewar wani mazauni garin Abdullahi Isah da ke jinya yanzu haka kan harbin ‘yan bindiga.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply