Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Hasken lantarkin Nijeriya ya ƙaru da megawat 5,552 – TCN

Hasken lantarkin Nijeriya ya ƙaru da megawat 5,552 – TCN

92
0

An samu karuwar hasken lantarki zuwa megawatt 5,552 a Nijeriya, a ranar Larabar da ta gabata, kuma kamfanin raba hasken lantarkin TCN ya yi nasarar bada lantarkin a fadin kasar.

Wata sanarwa da manajan harkokin yau da kullum na kamfanin Ndidi Mbah ya fitar a ranar Alhamis, ya ce lantarkin da kamfanin ya samar ya zarta wadda aka samar a watan Oktobar bara na megawatt 5,520 da kimanin megawatt 32.40.

Sanarwar ta kuma ce wannan ci gaba, alama ce da ke nuna tsayuwar hasken lantarki da ke samuwa a hankali, karkashin jagorancin gwamnati mai ci.

Sanarwar ta kara da cewa duk da karfin da TCN ke da shi na raba megawatt 8,100, amma ya yi nasarar raba hasken lantarkin a bisa karfin gudun 50.08Hz.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply