Home Labarai Hassada ta sa Ganduje tsige Sarki Sanusi – Kwankwaso

Hassada ta sa Ganduje tsige Sarki Sanusi – Kwankwaso

172
0

Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bayyana hassada a matsayin dalilin da ya sa Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige Sarki Muhammadu Sanusi II daga kujerarsa.

Kwankwaso wanda ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Sakatarensa Muhammad Inuwa Ali ya fitar a ranar Talata, ya ce Ganduje na baƙin ciki da duk wani abu da Sanusi ke da shi, kama daga ilimi, gogewa, tunanin ci gaba, da kuma soyayyar talakawa.

Ya ƙara da cewa suna sane da yadda Gandujen ya ɗora karan tsana ga tsarin sarautar Kano da kuma ƙoƙarinsa na ganin ya warware duk wani abu da Kwankwason ya yi.

Wannan dai na a matsayin martani ne ga iƙirarin da Ganduje ya yi a lokacin ƙaddamar da wani littafin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

A lokacin dai Ganduje ya ce an naɗa Sanusi a matsayin sarki ne domin a baƙanta wa Jonathan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply