Home Labarai Hatsarin mota ya kashe mutum 13 a Katsina

Hatsarin mota ya kashe mutum 13 a Katsina

54
0

Akalla mutum 13 sun rasu, wasu da dama kuma suka samu munanan raunuka a hatsarin da ya ritsa da wata tirela a hanyar Kaita zuwa Dankama a Jihar Katsina.

Hatsarin ya auku ne a yayin da babbar motar dabbobin kirar Iveco da ta dauko mutanen ta kama hanyar zuwa Legas a daren Alhamis.

Shaidu sun ce gudun wuce ka’ida ne ya yi sanadiyyar kwacewar motar da ta fadi bayan barowarta Kasuwar kan iyaka da ke Dankama, nan take kuma dabbobi 70 suka hallaka.

Mataimakin shugaban ƴan kasuwar dabbobi na Jamhuriyar Nijar a jihar, ya bayyana kaduwarsa da rashin da aka yi, inda ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Katsina da ta dauki nauyin kula da wadanda suka samu rauni da kuma jana’izar mamatan.

Tawagar gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin kwamishinan kananan hukumomi, Ya’u Umar Gwajo-gwajo ta yi wa iyalan mamatan ta’aziyya tare da addu’ar samun rahama gare su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply