Wani mummunan hatsarin mota da ya wakana a jihar Sokoto, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11.
Hadarin dai ya faru ne a kwanar Kawadata fita wajen garin Goronyo na jihar Sakkwato kan hanyar su ta zuwa Lafia babban birnin jihar Nasarawa.
Mutanen da suka rasa rayukansu maza uku da kuma mata bakwai har da direban motar da ta kwace masa ya yin da ya ke kokarin shiga wata kwana.
An gudanar da sallar jana’izar mutanen kamar yadda Addinin Islama ya tanada.
