Home Labarai Hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 a Katsina.

Hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 a Katsina.

77
0

Wani hatsarin mota a daren Lahadin nan, kan hanyar Mai’adua zuwa Shargalle ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17, wasu 14 suka samu ranunuka daban-daban a Katsina.

A wata takarda daga mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar SP Gambo Isah, ta ce motar kirar DAF ta yo lodin shanu ne daga Kasuwar Mai’adua zuwa jihar Legas.

Takardar ta ce, DAF din na tafiya ne, sai kan ta ya cire, bodin ya fada cikin wata gada da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da jikkatar sauran.

Daga nan ne aka garzaya da su asibitin garin Mashi, inda daga nan aka tabbatar da mutuwarsu.

Takardar ta ce kwamishinan ‘yansandan jihar Katsina CP Sanusi Buba na ta’aziyya tare da jajanta wa al’ummar jihar Katsina bisa faeuwar wannan ibtila’i.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply