Kungiyar Boko Haram sun dauki alhakin sace daruruwan’ yan makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati, da ke Kankara a jihar Katsina a wani hari da aka kai a ranar Juma’ar da ta gabata da daddare.
A cikin waini sauti da shugaban Boko Haram ya fitar ya ce sun yi hakan ne sakamakon yadda suke adawa da karatun boko.
