Home Sabon Labari HISBAH a Kano za ta kai wasu almajirai  kotu saboda sun yi...

HISBAH a Kano za ta kai wasu almajirai  kotu saboda sun yi bara

66
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

Hukumar HISBAH a jihar Kano ta ce ta kama almajirai 146 da ke yawon bara a cikin kwaryar birnin Kano bisa zargin karya dokar da gwamnatin jihar ta saka kan hana barace-barace.

Mukaddashin Darakta Janar na hukumar Dr Aliyu Musa ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Kano.

Dr. Aliyu Musa ya sanar da cewa mabaratan sun hada da manya 114 da kananan yara 52, ya kara da cewa an kama su ne a ya yin samame daban-daban da aka kai a cikin birnin na Kano.

Yace an kama almajiran ne wajen karfe 12:00 na dare zuwa karfe 4:00 na asuba a wurare daban-daban da suka hada da Gadar Bata, kasuwar Kantin Kwari, Railway da kasuwar Wambai da dai sauransu.

Gwamna Ganduje na jihar Kano

Mukaddashin Darakta Janar na hukumar ya ce daga cikin mabaratan 146 da aka kama, 77 daga cikinsu ‘yan Kano ne, sai 69 daga jihohin Abia, Adamawa, Borno, Ekiti, Jigawa, Gombe, Zamfara da Jamhuriyar Nijar da dai sauransu.

Ya kara da cewa daga cikin su akwai mabarata da mata 3 masu tabin hankali, inda ya ci gaba yana cewa hukumar za ta tantance ta saki wadanda aka yi wa kamen farko, sannan ta mika wadanda aka taba kamawa a gaban kotu.

Dr. Aliyu Musa, ya roki mabarata da su rika amfani da baiwar da Allah Ya huwace musu su kama sana’o’in hannu don su dogara da kansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply