Home Labarai Hisbah ta kama mabarata 178 a Kano

Hisbah ta kama mabarata 178 a Kano

137
0

Hukumar Hisbah a Kano ta ce ta kama
mabarata 178 da suka karya dokar hana bara da gwamnatin jihar ta saka.

Hukumar kamar yadda babban kwamandanta Harun Ibn-Sina ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Kano, yace hukumar ta yi wannan kamen ne daga watan Satumba zuwa Disambar nan.

Yace daga cikin wadanda suka kama akwai mata 102 da maza 76. Ya kara da cewa hukumar za ta cigaba da kamen duk mabaratan da suka yi kunnen kashi game da dokar hana bara ta gwamnatin Kano.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply