Home Labarai Hisbah ta kama mabarata 646 a Kano

Hisbah ta kama mabarata 646 a Kano

111
0

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama mabarata 648 a cikin kwaryar birnin Kano da ake zargin sun karya dokar hana bara da gwamnatin jihar ta kafa daga watan Fabrairu zuwa yanzu.

Mai magana da yawun hukumar Lawal Ibrahim ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Kano, inda ya ce an kama wadanda ake zargin ne a Bata, kan titin Murtala.

Ya ce wadanda aka kama din sun hada da maza 416 da mata 232.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply