Home Labarai Horas da Kangararru:Yan sanda sun dira a makarantar Malam Niga

Horas da Kangararru:Yan sanda sun dira a makarantar Malam Niga

67
0

Yan sanda a ranar Larabar nan sun dirar wa gidan horas da kangararru na Malam Niga da ke Katsina.

Rahotanni sun ce an turo yan sandan ne zuwa Katsina daga Abuja.

Kawo yanzu kuma sun yi awon gaba da wasu cikin malaman makarantar.

Gidan rediyon Deustche Welle ya ce ‘yan sandan da suka kai samame makarantar, sun ce sun kubutar da maza da yara masu kananan shekaru da ake daure dasu da mari ko sarka, wasu daga cikinsu, sun shedawa musu halin da suka kasance na tsananin azaba tun bayan da suka sami kansu a makarantar.

Wannan na zuwa ne kwana guda da kubutar da wasu mutum kusan saba’in ‘yan shekara tsakanin bakwai zuwa arba’in a wata makarantar Islamiya da ke garin Daura a jihar ta Katsina.

Kawo yanzu mutum dubu daya aka kubutar daga ire-iren wadannan makarantu da iyaye ke kai yara kangararru don gyara musu tarbiya a yankin Arewacin Najeriya.

Bayan samamen na Daura da ya kasance mahaifar Shugaban kasar,  ya soma fuskantar matsin lamba kan daukar matakin gaggawa don gano dubban yaran da ake zaton na watse a wasu makarantun a Najeriyan.
 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply