Home Labarai Hoto: Buhari ya saka takunkumi kafin halartar taron majalisar zartarwa

Hoto: Buhari ya saka takunkumi kafin halartar taron majalisar zartarwa

32
0

Yanzu haka shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Taron na gudana ne a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja, kuma shi ne na farko a wannan watan na Fubrairu.

A wajen taron dai Buhari ya saka takunkumin kariya daga Covid-19 wanda ba kasafai ake ganin yana yin hakan ba.

A ranar Talata ne dai shugaban ya dawo daga Daura mahaifarsa inda ya kai ziyarar sabun ta rajistarsa ta jam’iyyar APC da ta janyo cecekuce, saboda shugaban ya shiga taron jama’a ba tare da takunkumin kariya ba, kwanaki kaɗan bayan sa hannu ga dokar da ta tilasta sa takunkumin a ko ina mutum zai je cikin ƙasar.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply