Home Wasanni Hoto: Tawagar ƙungiyar Wikki Tourist ta yi haɗari

Hoto: Tawagar ƙungiyar Wikki Tourist ta yi haɗari

33
0

Ƴan wasa da jami’an ƙungiyar ƙwallon ƙafar Wikki Tourist ta Bauchi sun yi hatsarin mota da safiyar ranar Alhamis ɗin nan.

Rahotanni sun nuna tawagar ƴan wasan na hanyarsu ta zuwa Birnin Uyo na jihar Akwa Ibom domin buga wasan Firimiyar Nijeriya, lokacin da suka samu hatsarin a Hawan Kibo da ke jihar Plateau.

Wikki Tourist za ta fafata ne da ƙungiyar Dakkada a ranar Asabar.

Sakataren ƙungiyar Abdullahi Ibrahim ya tabbatar da faruwar haɗarin ga ƴanjarida a Bauchi, yana mai cewa tayar motar da tawagar ke ciki ne ta fashe yayin da motar ta kama da wuta, saidai ya ce jami’ai da ƴan wasan ƙungiyar sun tsira ba tare da samun rauni ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply