Home Kasashen Ketare Huce haushi: Trump ya kori sakataren tsaron Amirka

Huce haushi: Trump ya kori sakataren tsaron Amirka

130
0

Shugaba Donald Trump na Amirka ya kori sakataren tsaron ƙasar Mark Esper, bayan saɓanin da aka riƙa samu a tsakaninsu.

Trump wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, ranar Litinin ya kuma ayyana Daraktan cibiyar yaƙi da ta’addanci na ƙasar Christopher Miller a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan mataki dai na zuwa ne watanni biyar bayan sakataren tsaron ya ƙi bin umarnin Trump na jibge jami’an soji su fatattaki masu zanga-zangar kare baƙaken fata ta Black Lives Matter a faɗin ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply