Home Labarai HUK Poly Katsina ta saka ranar komawar ɗalibai

HUK Poly Katsina ta saka ranar komawar ɗalibai

270
0

Kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina, ta sanya ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a ci gaba da harkokin koyo da koyar wa a kwalejin.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Ahmadu Umar, mai taimakawa maga-takardan kwalejin ya fitar, mai ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Oktoba, 2020.

Sanarwar ta ce hukumar kwalejin ta amince da makonni 3 don yin bitar darussa kafin fara jarabawar farko ta zangon karatun shekarar 2019/2020, yayin da kuma mataki na biyu na zangon karatun zai ci gaba da zaran an kammala jarabawar zangon farko.

Sanarwar ta kuma yi kira ga ɗalibai, malamai da sauran ma’aikata su kiyaye ƙa’idojin Covid-19 a lokacin da suke cikin kwalejin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply