Home Labarai Hukuma ta kama gidajen da ake ɓoye kayan abinci a Kano

Hukuma ta kama gidajen da ake ɓoye kayan abinci a Kano

193
0

Hukumar sauraron ƙorafin jama’a da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano ta ce ta zagaye wasu gidajen ajiyar kaya da aka ɓoye kayan abinci.

A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Muhuyi Rimin Gado ya fitar a ranar Laraba ya ce daga cikin kayan da aka samu a gidajen sun haɗa da buhu 19,500 na fulawa, buhu 5,120 na sukari, sunƙi 79,645 na Taliya da kuma sunƙi 37,000 na Makaroni.

Rimin Gado ya ce an ƙwace kayan ne a wani samame da jami’an hukumar suka kai a kasuwar Singer.

Hukumar dai tun da farko ta gargaɗi ƴan kasuwar da ke ɓoye kaya da nufin tsawwalawa jama’a da su dakata ko kuma hukumar ta ƙwace kayan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply