Home Labarai Hukumar JAMB ta saka ranar fara zauna jarabawar ta 2020

Hukumar JAMB ta saka ranar fara zauna jarabawar ta 2020

80
0

Abdullahi Garba Jani

Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a ta Nijeriya JAMB, ta saka ranakun 14 ga watan Maris da 4 ga watan Afrilu na 2020 a matsayin ranakun zauna jarabawar.

Hukumar ta ce za a zauna jarabawar tantancewa ta “Mock” ne a 18 ga watan Fabrairun 2020.

Shugaban hukumar Prof. Ishaq Oloyede ne ya sanar da hakan a lokacin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja, a inda ya gana da kwamishinonin ilmi na jihohi 36 na kasar.

Shugaban hukumar ya ce za a fara rajistar zauna jarabawar ne a ranar 13 ga watan Janairu, a kammala 17 ga watan Fabrairu, 2020.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply