Home Labarai Hukumar kwastan a Nijeriya ta kwace motoci 1,072

Hukumar kwastan a Nijeriya ta kwace motoci 1,072

79
0

Rahma Ibrahim Turare/Jani

Hukumar hana fasa-kwauri ta Nijeriya kwastan, ta ce ta kwace motoci akalla 1,072 daga ‘yan sumogal tun lokacin da aka rufe iyakokin kasar.

Mai magana da yawun hukumar Mista Joseph Attah ya sanar da hakan a katsina, a lokacin shirin fadakarwa a kan tsare-tsaren hukumar a kan iyakokin kasar.

Ya ce an kama motocin a lokacin da ake shirin shiga da su a kasar ta barauniyar hanya.

Ya ce sama da buhunan shinkafa ‘yar waje 19,000 da jarkokin man fetur 4,765, tare da tankar man fetur 2 aka kama. Attah ya kara da cewa an kama dubban makamai tare da wadanda ake zargi da aikata laifuka akalla mutane 317 .

Ya ce an kama buhunan taki samfurin NPK 131 wadanda ake shirin yin amfani da su wajen hada bama-bamai, a ya yin da kuma aka damke masu gudun hijira ba bisa ka’ida ba wadanda ba su da sahihan takardun tafiye-tafiye.

Ya bayyana cewa rufe kan iyakokin kasar da a ka yi ya taimaka kwarai da gaske wajen tabbatar da tsaro da kuma habaka tattalin arzikin kasar baki daya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply