Home Labarai Hukumar Kwastan ta kama kayan da dutin su ya haura ₦176m

Hukumar Kwastan ta kama kayan da dutin su ya haura ₦176m

122
0

Jami’an hukumar hana fasa ƙwabri ta Nijeriya shiyyar B da ke Kaduna sun ƙwace kayan da kuɗin harajin su ya kai ₦176,976,600.

Mai magana da yawun hukumar ASC Malam Abubakar Usman ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa ƴan jarida bayani a Kaduna.

Ya ce daga ciki akwai motoci da ke ɗauke da shinkafa buhu 249 da aka ɓoye cikin buhunan wake, da Tirela mai ɗauke da buhu 125 na shinkafa da aka ɓoye cikin buhunan masara da kuma wata Tirelar kankana da aka saƙa buhu 119 na shinkafa a ciki.

Sauran sun haɗa da wata tirela ɗauke da dila 63 ta kayan sawa da bandir 284 na shadda da buhun taki 213.

Usman, wanda ya tabbatar da kuɗin harajin kayan sun kai ₦176,976,600, ya ce an kama su ne a Funtua ta jihar Katsina da kuma Kebbi.

Ya ƙara da cewa an kama mutum huɗu da ake zargin suna da alaƙa da safarar kayan kuma ana gudanar da bincike a kan su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply