Home Labarai Hukumar Kwastan ta kama sama da tirela 52 ta aya da dabino...

Hukumar Kwastan ta kama sama da tirela 52 ta aya da dabino a Katsina

57
0

Hukumar hana fasa kwabri ta Nijerya ta yi nasarar kama sama da tirela 52 ta aya da dabino da aka yi yinkurin shigowa da su a Katsina, a wani sintirin hadin gwiwa da hukumar ta gudanar.

Hukumar ta yi zargin cewa motocin na dauke da wasu kayan da aka hana shigowa da su kasar, da suka hada da shinkafa, da kwayoyi, da alburusai.

Zargin da masu sayar da aya da dabinon suka musanta.

‘Yan kungiyar masu sayar da aya da dabino, da wasu jama’a ne suka shaida yadda hukumar ke tantance motocin da ta kama.

Sama da makonni uku kenan ana fuskantar karancin aya da dabino wadanda aka fi samu a yankin Arewacin Nijeriya musamman Katsina.

Yanzu haka dai, ba a cika samun kayan a kasuwa ba, saboda yadda aka takaita zirga-zirga a kan iyakokin kasar na kan tudu.

Aya da dabino dai na da matukar tasiri ga rayuwar jama’ar Arewacin Nijeriya, musamman a wannan lokaci da dabino ke neman maye gurbin goro, a lokacin bukukuwa.

Mukaddashin kwamandan hukumar ta sashe na hudu mai kula da kan iyakoki, Muhammad Aliyu, ya ce ba wai ana wannan aiki don muzgunawa wasu ba ne, saidai don tabbatar da ba a shigo da kayan da aka hana shigowa da su ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply