Home Labarai Hukumar kwastan za ta kashe N238bn a 2020

Hukumar kwastan za ta kashe N238bn a 2020

73
0

A jiya ne Majalisar dattawa ta amince da kasafin kuɗin Hukumar kwastan na shekarar 2020 da ya kai N238bn.

Wannan ya biyo bayan rahoton kasafin Hukumar, da shugaban kwamitin Majalisar Francis Alimikhena ya gabatar.

Daga cikin kuɗin za a kashe N98bn kan ma’aikata, sai N15bn na ko ta kwana da kuma N123bn na manyan ayyuka.

Kasafin dai ya nuna Hukumar za ta kashe N128mn wajen sayen talabijin yayinda zubar da shara zai laƙume N3.1bn sai gina rijiyoyin burtsatse da aka warewa N577m.

Kafin Majalisar ta amince da kasafin, saida wasu sanatoci suka nuna rashin amincewa da shi.

Suna masu cewa rahoton kwamitin bai bada cikakkun bayanai ba.

Sai dai kuma shugaban Majalisar Ahmad Lawan, ya yi gargaɗin ɗaukar matakin ladabtarwa ga hukumomin gwamnati da ba su binciken yadda ake kashe kuɗaɗen su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply