Home Sabon Labari Hukumar NDLEA ta banka wa kadada 10 ta gonar tabar-wiwi wuta a...

Hukumar NDLEA ta banka wa kadada 10 ta gonar tabar-wiwi wuta a jihar Kogi

68
0

Abdullahi Garba Jani

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA  ta ce ta lalata kadada 10 ta gonar tabar wiwi a jihar Kogi.

 

Hukumar ta ce wannan aikin na daga cikin kokarinta na kakkabe yawaitar kwayoyin da abubuwan da ke sa maye a jihar.

 

Da sanyin safiyar Alhamis din nan ne jami’an hukumar suka kai samame a yankin Igolijo na Karamar Hukumar Igalemela-Odolu, inda suka kama wani da ake zargi da mallakar gonar mai suna James Ameh da karin wasu mutane 6.

 

Tawagar hadin guiwar hukumar ta NDLEA da jami’an tsaron farar hula na Civil Defence sun yi nasarar kama babban madugun da ake zargi da masu taimaka masa su 6.

 

Mutanen 6 da su ma ake zargi su ne, Eze Stanley, Innosent Ameh, Ojima Ojo, Ekene Ukwueze, Usman Bello da Samule Idoko. Amma Mr Ameh ya musanta mallakar gonar mai fadin murabba’in kadada 10 ta tabar-wiwi duk kuwa da an sha ganinsa cikinta.

 

Jaridar Daily Nigerian ta ba da rahoton cewa hukumar NDLEA ta banka wa gonar wuta inda ta kone kurmus.

 

Shugaban hukumar ba jihar Kogi  Idris Bello ya ja kunnen cewa duk wanda suka kama yana tu’ammali ko safarar kwayoyi, to kuwa ya kuka da kansa.

 

 

Daily Nigerian:    Jani/dkura

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply