Home Labarai Hukumar NDLEA ta yi kame ta kuma kwace kilogram 30 na tabar...

Hukumar NDLEA ta yi kame ta kuma kwace kilogram 30 na tabar wiwi a Nijeriya

68
0

 Abdullahi Garba Jani

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA a babban birnin kasar Abuja ta ce ta kama mutane 49 da take zargin da sayar da kwayoyi.

 

Kazalika, hukumar ta ce ta amshe kilogram 30 na muggan kwayoyi daga wajen wadanda ake zargin a watan Agustan da ya wuce.

 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Mr Peter Adegbe ne ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN a Abuja. Mr Adegbe ya ce daga cikin kwayoyin da suka kwace sun hada da Tramadol , Codeine , da Shalasha mai tarin yawa.

Tabar wiwi a Nijeriya

Mr Peter ya ce sun yi wannan samame ne da suka yi wa lakabi da “Shara” da ke da zummar shawo kan matsalar sayar da kwayoyi barkatai.

 

Ya ce ya zuwa yanzu rundunar ta fara samun nasarori ta yadda har ta fara gurfanar da wasu da aka kama a gaban kotu don fuskantar shari’a inda aka gyara dabi’un wasunsu da dama. Sai dai kuma wannan hukuma ta NDLEA wasu ‘yan Nijeriya na zarginta da sakaci wurin aiwatar da ayyukanta da kuma mayar da hankali akan talakawa kawai a maimakon kowane dan aksar da ke ta’amalli da kwayoyi.

 

Sai dai jami’in hulda da jama’ana hukumar  ya ce za a ci gaba da wannan sintiri mai lakabin “Shara” har karshen wannan watan na Satumba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply