Home Coronavirus Hukumar NIMC ce ta fi dacewa da rabon kayan tallafin Covid-19 –...

Hukumar NIMC ce ta fi dacewa da rabon kayan tallafin Covid-19 – Asekokhai

195
0

Shugaban kungiyar kwadago reshen hukumar samar da katin dan kasa NIMC Lucky Asekokhai, ya ce hukumar ce ya dace a barwa aikin rabon kayan tallafi ga ‘yan Nijeriya masu karamin karfi.

A cikin wata sanyara da ya fitar a jiya Lahadi Asekokhai ya ce ya kamata hukumar ta shigo cikin aikin rabon kayan, saboda ita ce za ta iya bada sahihan bayanai na hakikanin ‘yan Nijeriya masu karamin karfin.

A cewar sa yin amfani da lambar banki ta BVN bai isa ya tantance ‘yan Nijeriyar ba, domin ‘yan kasar miliyan 40 ne kacal suka mallake ta, kuma mafi yawancin talakawan kasar ba su da asusu a bankin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply