Home Labarai Hukumar “NIMC” ta koma karkashin ma’aikatar sadarwa

Hukumar “NIMC” ta koma karkashin ma’aikatar sadarwa

206
0

Gwamnatin Nijeriya ta amince da mayar da hukumar da ke samar da katin zama dan kasa NIMC karkashin kulawar ma’aikatar sadarwa da inganta tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani.

Hajiya Uwa Suleiman ita ce mai magana ya yawun ma’aikatar sadarwa da inganta tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani ta bayyana haka a Abuja.

Amincewar ta biyo bayan la’akarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi game da irin alakar da ta ke tsakanin ma’aikatun biyu.

Uwa Suleiman ta bayyana cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da hadin guiwa da kuma taimakekeniya wajen yadda za a kawo sauye-sauyen zamani a hukumar ta NIMC.

Kafin wannan mataki, hukumar ta NIMC na a karkashin kulawar ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply