Home Labarai Hukumar NYSC ta gargadi masu shirya fina-finai kan amfani da kakinta

Hukumar NYSC ta gargadi masu shirya fina-finai kan amfani da kakinta

309
0

Hukumar da ke kula da matasa masu yi wa kasa hidima NYSC, ta bukaci masu shirya fina-finai a Nijeriya da su rika neman amincewarta idan za su yi amfani da kakin ‘yan bautar kasa a fina-finansu.

Mista Christian Oru, mataimakin darakta a sashen dokoki ya fadi haka a Legas ya yin wani taro tsakaninsu da hukumar shirya Fina-finan ta Kasa da kuma hukumar tace Finafinai a jihar Legas.

Hukumar ta NYSC ta ce ba za ta sake lamunta ba masu shirya fina-finai a fadin kasar su cigaba da yin amfani da inifam din ta cikin fina-finai ba tare da izini ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply