Home Sabon Labari Hukumar Road Safety a Nijeriya ta  kama masu karya dokar tuki

Hukumar Road Safety a Nijeriya ta  kama masu karya dokar tuki

79
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa a jihar Enugu ta ce ta kama mutane 1,396 da laifukan karya dokar tuki a jihar cikin wannan shekara ta 2019.

Kazalika, hukumar ta kuma yi kamen laifuka 1,484 a jihar Enugu duk a cikin wannan shekara.

Shugaban hukumar na jihar Enugu Mr. Ogbonnaya Kalu ya fada wa kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya _NAN_ a birnin Enugu cewa hukumar ta gurfanar da mutane 136 da aka kama da laifuka daban-daban a gaban kotu, tun a watan Janairun wannan shekara ta 2019.

Mr Kalu ya ce ana iya samun mutum daya da laifukan da suka zarta 2-3.

Sai kuma yace hukumar ta samar da lasisisin tuki 13,634 duk a shekarar 2019.

Mr. Kalu ya yi kira ga mutane da su rika bin dokoki da ka’idojin tuki don gujewa afkuwar hadurra.

Sai dai wasu  yan Nijeriya na sukar yadda wannan hukuma ta Road Safety ke gudanar da ayyukanta. Wasu na zargin jamian hukumar sun fi mayar da hankalinsu wurin kama mai laifi ba wai lafiyar direba ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply