Home Sabon Labari Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta kwato Milyan 256 a...

Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta kwato Milyan 256 a 2019

187
0

Shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da karbar rashawa a jihar Kano Alhaji Muhyi Magaji ya ce shekarar 2019 ta kasance babba a gare su. Ya ce sun sami korafi na cin hanci da jami’ai ke yi fiye da shekarar 2018.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya-NAN- ya ruwaito Magaji na cewa a tsakanin watan Janairu na 2019 zuwa Disamba sun kwato kudaden da suka kai Naira Milyan 256. Akwai gidaje fiye da 100 da suka kwace ga kuma filaye. Dukkansu acewarsa an kwato su daga wurin jami’an da hukumarsu ta tuhuma a kotu sakamakon karkatar da dukiyar gwamnati ko kuma jama’a.

Magaji ya ce sun sami korafe-korafen cin hanci da suka kai 3,192 kuma kawo karshen shekarar da ta gabata sun yi nasarar warware korafi 1,858. Sai dai ya ce akwai wadanda suka nemi a yi sulhu da su a wajen kotu yayinda wasu korafe-korafen ke a gaban kotu yanzu haka.

Shugaban hukumar yaki da cin hancin ya ce wannan babbar nasara da suka samu ta kwato kudade da gidaje da filaye ta samu ne a sakamakon goyon baya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke ba su wurin kawar da cin hanci da hana karbar rashawa a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply