Home Labarai Hukumomi na binciken silar tashin gobara a ofishin INEC na Ondo

Hukumomi na binciken silar tashin gobara a ofishin INEC na Ondo

132
0

Ƴan sanda na aiki da jami’an hukumar zaɓen Nijeriya INEC a jihar Ondo, don binciken musabbabin tashin gobara a ofishin hukumar da ke Akure, a makon jiya.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Ondo Salami Amidu Bolaji, ya bayyana tashin gobarar a magsayin abun takaici, saidai ya ce ba da daɗewa ba za su gano dalilin faruwar ta.

Wutar wadda ta yi silar ƙonewar na’urar tantance masu zaɓe (card reader) 500, ta tashi ne a ranar 9 ga watan Satumba da misalin 7:30pm na yamma a shelkwatar hukumar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply