Home Sabon Labari Ibrahimovic ya kafa sabon tarihin cin ƙwallaye

Ibrahimovic ya kafa sabon tarihin cin ƙwallaye

26
0

Zlatan Ibrahimovic ya karya tarihin cin kwallaye 500 a wasan kungiyoyi, bayan kwallaye biyu da ya ci, wadanda suka ba AC Milan damar sake dare wa teburin Serie A, a wasan da suka doke Crotone da ci 4-0 a ranar Lahadi.

Milan ta koma saman teburin ne tare da tazarar maki biyu da ta ba abokiyar hamayyarta Inter Milan da suka shiga gaba bayan sun yi nasara kan Fiorentina da ci 2-0 a ranar Juma’a, sai kuma Juventus da ke rike da kofin suke matsayi na uku bayan sun doke Roma suma da ci 2-0 a wasansu na ranar Asabar.

Ibrahimobic dan shekara 39, ya ci kwallonsa ta 500 ana minti na 30 da fara wasan, sannan ya ci ta 501 kuma ta 83 a Milan, ana mintuna na 64 da take ledar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply