DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeBinciken Gaskiya (Fact Check)ICPC ta gano ma’aikatan bogi 908 a ma’aikatun gwamnatin Nijeriya

ICPC ta gano ma’aikatan bogi 908 a ma’aikatun gwamnatin Nijeriya

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC a Nijeriya ta gano ma’aikatan bogi 908 a akalla ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 50, inda ta ce an gano cewa an biya kusan Naira miliyan 942 a matsayin albashin bogi.

Shugaban hukumar ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN), ne ya bayyana hakan yayin da yake magana kan binciken da hukumar ke gudanarwa kan zamba da ake zargin an yi a tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati, kamar yadda BBC Pidgin ta ruwaito.

A cewar hukumar, ma’aikatan bogi su ne mutanen da aka saka sunayensu a cikin tsarin biyan albashin gwamnati ba tare da suna aiki a hukumomin da aka sanya su ba.

Jaridar Punch ta ruwaito a wasu lokuta kuma, ana zargin wasu jami’ai da saka sunayen ’yan uwansu ko abokansu cikin jerin ma’aikata domin karbar albashinsu.

Hukumar ta ce rundunar ’yan sandan Nijeriya ce ta fi yawan ma’aikatan bogi da aka gano, inda aka gano mutane 570 da ake zargin suna karbar albashi ba tare da yin aikin da aka dauke su ba.

Hukumar Kula da albarkatun ruwa ta kasa ce ta biyo baya da mutane 80 da ake zargin ma’aikatan bogi ne, yayin da ma’aikatar ayyuka ta tarayya ke da 56.

Haka kuma, an gano ma’aikatan bogi 24 a ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, 19 a ma’aikatar tsaro, sannan ma’aikatar wutar lantarki ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari kowacce tana da mutane 17 da ake zargin ma’aikatan bogi ne.

Bugu da kari, an gano mutane 15 da ake zargin ma’aikatan bogi ne a ma’aikatar lafiya ta tarayya, yayin da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ke da mutane 12.

Shugaban ICPC ya kuma bayyana cewa binciken ya gano wani mutum da ake zargin ya saka sunayen matarsa, dansa da kuma surukarsa cikin jerin ma’aikatan gwamnati, yayin da shi ma yake karbar albashin wasu ma’aikata 12.

ICPC ta ce binciken da ta fara a shekarar 2024 kan zamba da ake yi ta hanyar tsarin albashin gwamnati na ci gaba, yayin da ake kokarin gano sauran ma’aikatan bogi da kuma wadanda ke da hannu wajen almundahana da kudaden gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata