Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ICPC ta ce ta bankado wata badakalar bilyoyin kudi a asusun bai daya na TSA a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Nijeriya.
Shugaban hukumar Prof Bolaji Owasanoye ne ya furta hakan, a jawabinsa na taron yaki da rashawa karo na 2 a Abuja.
Taron ya samu halartar shugaban kasa Buhari, Mai Shari’a Tanko Muhammad da kuma shugaban Kungiyar gwamnonin Nijeriya Dr Kayode Fayemi da sauran jiga-jigan gwamnati.
