Home Sabon Labari Idan aka ci gaba da tsorata mu za mu koma Abuja-Kotun Zaben...

Idan aka ci gaba da tsorata mu za mu koma Abuja-Kotun Zaben Kano 

77
0

Abdullahi Garba Jani

 

Kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano ta yi barazanar komawa Abuja da zama muddin aka yi barazana ga rayuwar wani daga cikin mambobinta.

Shugabar zaman sauraron karar mai shari’a Halima Muhammad ce ta fadi haka a lokacin da take Allah-wadai da yunkurin kai farmaki ga daya daga cikin shaidun da suka bayyana gabanta da ya ba da shaida game da hukumar zabe ta Nijeriya -INEC- kan karar.

Mai shari’a Halima Muhammad tace ita ce wadda ta nace cewa sai kotun ta yi zamanta a Kano don ba al’ummar Kano damar gani da jin abubuwan da kotun ke aiwatarwa.

Ta ce idan kotun ta koma da zamanta a Abuja, sai dai Kanawa su rika tsintar labari a rediyo da sauran kafafen watsa labarai.

Yunkurin komawa Abuja da zaman sauraron kararrakin zaben ya biyo bayan koken da lauyan -INEC- Mr Adedayo Adedeji ya ce akwai barazanar da aka yi wa wata shaida mai suna Halima Sambo Hassan a kafar sadarwa soshiyal midiya. An dai dauki hoton Halima Hassan wadda ita ce babbar jami’ar hukumar zabe a karamar hukumar Ungoggo da ke jihar aka saka a soshiyal midiya ake alakanta ta da gwamnati wadda wasu suka ci gaba da jefa mata munanan kalamai.

Sai dai da ya ke magana kan batun, lauyan PDP Maliki Kuliya Umar ya bayyana lamarin da yi wa doka karan-tsaye, da ya ce hakan ba za ta sabu ba.

Jaridar Daily Trust ta ba da rahoton cewa mai shari’a Halima Muhammad ta ba hukumomin da abin ya shafa umurnin da su binciki làmarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply