Home Labarai Idan har za a iya harin gwamna, rayuwarmu babu tabbas – Shehun...

Idan har za a iya harin gwamna, rayuwarmu babu tabbas – Shehun Borno

347
0

Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi ya koka da cewa har yanzu jihar Borno babu zaman lafiya, bayan harin da aka kai wa tawagar gwamna Babagana Zulum.

Shehu ya yi wannan kukan ne a lokacin da ya kai wa gwamnan ziyarar gaisuwar sallah a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Maiduguri da yammacin ranar Juma’a.

A ranar Laraba ne dai aka kai wa tawagar gwamnan hari a garin Baga da ke ƙaramar hukumar Kukawa lokacin da ya ziyarci yankin.

Elkanemi ya ce ba su ji daɗin abun da ya faru ba, yana mai cewa idan har za a kai wa gwamna mai matsin lamba ɗaya kuma shugaban tsaro a jihar, to babu wanda zai kwana da tabbacin rayuwarsa na cikin tsaro.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply