Manchester United sun bada sanarwar tsawaita zaman aron da dan wasan gaban Nijeriya Odion Ighalo ke yi a kungiyar.
A ranar Litinin ne United ta sanar da tsawaita yarjejeniyar a shafin ta na intanet.
Sanarwar ta ce kungiyar ta cimma yarjejeniya da kungiyar Shanghai Greenland Shenhua don tsawaita zaman Ighalo a kungiyar.
Zaman Ighalo a United dai yak are ne a ranar 31 ga watan Mayu, saidai yanzu zai kasance a kungiyar har zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2021 domin kara kafuwa kan kyakkyawar shigar da ya yiwa kungiyar da yake goyon baya tun a yarintar sa.
Ighalo dai ya ci kwallaye hudu a wasanni 8 da ya bugawa United.
Kungiyar ta kara da cewa tabbacin zaman Ighalon wata dama ce da Ole Gunnar Solskjaer zai kara karfafa ‘yan wasan da a daidai lokacin da wasanni za su dawo a Ingila.
Duk da cewa dai har yanzu Ighalo bai ce komai kan tsawaita zaman sa a United ba, amma dai ya rubuta a shafin sa na Twitter yana taya murnar shigowar watan Yuni a ranar Litinin.
